Majalisar dinkin Duniya tace fiye da rabin 'yan Najeriya basu samu abinci mai gina jiki a shekarar 2025 ba sakamakon karuwar Talauci da tsadar rayuwa

Majalisar dinkin Duniya ce dai ta fitar da wannan rahoto dake cewa fiye da 'yan Najeriya miliyan 191 ba su samu abinci mai gina jiki ba a shekarar 2025, sakamakon yana yin tsadar kayayyaki da kasar ke fuskanta.
Rahoton ya nuna cewa adadin mutanen da ba su iya biyan kuɗin abinci mai gina jiki ya ƙaru sosai daga miliyan 137.5 a shekarar 2017 zuwa miliyan 191.2 a shekarar 2025.
Rahoton majalisar dinkin Duniyar mai taken State of Food Security and Nutrition in the World 2026 ya kuma bayyana cewa mafi ƙarancin kuɗin da mutum zai kashe domin samun abinci mai gina jiki na yini daya a Najeriya ya tashi daga dala $2.78 zuwa dala $4.17 cikin shekaru takwas.
Kazalika Rahoton ya tantance yiwuwar samun abinci mai gina jiki ne bisa mafi ƙarancin kuɗin da ake buƙata domin sayen nau'ukan abinci da ake samu a cikin gida waɗan da za su cika dukkan buƙatun jiki na sinadirai.
A bangaren Africa kuwa rahoton ya bayyana cewa yanzu ta zarce Asiya a matsayin nahiyar da ke da mafi yawan mutanen da ke fama da yunwa, wadda aka kiyasta cewa mutane miliyan 309 a Afirka sun fuskanci yunwa a shekarar 2025.



