2027: Ba ta yadda za'a yi Kwankwaso da Obi su iya cin Kano - Ganduje
Usman Muhammad Ismail 0 views

Tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce tikitin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a ƙarƙashin jam'iyyar NDC ba zai yi nasara a jihar Kano ba a zaɓen 2027.
Ganduje ya bayyana cewa tikitin ba shi da ƙarfin siyasa da zai samu goyon bayan al'ummar Kano. Ya kuma soki tarihin shugabancin Peter Obi da Kwankwaso, yana mai cewa ba su nuna irin ƙwarewar da za ta sa su samu amincewar masu kaɗa ƙuri'a a jihar ba.



