Koma Labarai
Labarai

Hukumomin lura da yana yi sun sake yin gargadi kan yiwuwar ambaliyar Ruwa a jihar Jigawa da karin wasu jihohin 16.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Hukumomin lura da yana yi sun sake yin gargadi kan yiwuwar ambaliyar Ruwa a jihar Jigawa da karin wasu jihohin 16.

Duk da yana yin karancin Ruwa da wasu yankunan kasar nan ke fuskanta a Damunar bana, hukumar lura da yana yin Ruwa ta kasa ta fitar da wani sabon gargadin ambaliyar Ruwa na tsawon kwanaki 7.

Hukumar ta bayyana wannan gargadi ne biyo bayan karuwar wuraren sanya ido kan koguna, lamarin dake kara tabbatar da yiwuwar aukuwar ambaliya a yankunan dake kusa da Kogi da sauran wuraren da Ruwa da mamayewa.

Babban daraktan hukumar Umar Mohammed ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar gargadin a ranar Talatar nan.

Daga cikin jihohin da aka yi hasashen sun hada da Jihar Jigawa sai Kano da Kaduna da Kebbi da Bauchi sai Neja da Nasarawa da kuma Plateau da Taraba sai Yobe da Zamfara.

Sauran su ne Adamawa da Benue da Borno da Gombe da Edo da Imo, inda sanarwar gargadin tace tashoshin Auna Ruwa guda 16 a fadin kasar nan suna nuna matakan Ruwa sun yi yawa fiye da yadda aka saba gani.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM