Koma Labarai
Labarai

Hukumar tabbatar da ingancin abinci da magunguna NAFDAC ta fara aikin aiwatar da haramcin sayar da Giya a Leda da Kwalaben Roba

Usman Muhammad Ismail 0 views
Hukumar tabbatar da ingancin abinci da magunguna NAFDAC ta fara aikin aiwatar da haramcin sayar da Giya a Leda da Kwalaben Roba

Hukumar Lura da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta fara wani samame a faɗin kasar nan domin tabbatar da cikakken aiwatar da haramcin sayar da dukkan nau'ikan giya da ake zubawa a cikin leda da kuma kwalaben roba masu ƙasa da girman milimita 200.

Matakin ya zo ne bayan wa'adin da gwamnatin tarayya ta bayar ya kammala , inda hukumar ta ce daga yanzu za ta kama duk wanda aka samu yana samarwa, rarrabawa ko sayar da irin waɗannan kayayyaki da aka haramta.

NAFDAC ta bayyana cewa manufar haramcin ita ce kare lafiyar jama'a, musamman matasa, tare da rage yawan shaye-shayen giya da ke haddasa matsalolin lafiya da na zamantakewa.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM