Koma Labarai
Labarai

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya bayar da umarnin gaggauta samarwa da raba buhunan taki sama da miliyan uku ga manoma, domin tallafa musu wajen noman rani.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya bayar da umarnin gaggauta samarwa da raba buhunan taki sama da miliyan uku ga manoma, domin tallafa musu wajen noman rani.

Shettima ya bayar da umarnin ne a ranar Litinin, yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a harkar taki suka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Matakin ya biyo bayan amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da samar da kuɗaɗen gudanar da shirin gwamnatin tarayya na inganta noma da samar da abinci, domin rage farashin taki da ƙara yawan amfanin gona.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma umarci Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro da ya tabbatar da yawan takin da ake da shi, tare da sanya ido kan yadda za a raba shi ga manoma.

Ya jaddada cewa dole ne a tabbatar manoman da ke yankunan da ke fama da matsalolin tsaro, da waɗanda ke wurare masu wahalar isa, sun amfana da shirin.

Shettima ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu masana'antun haɗa taki a Najeriya ke aiki ƙasa da ƙarfinsu, duk da ƙaruwar buƙatar taki mai rahusa a ƙasar.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta sayi takin da masana'antun cikin gida suka samar, sannan ta sayar da shi ga manoma a farashi mai sauƙi.

A nasa ɓangaren, Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu, ya ce an gano kimanin tan 496,000 na taki da kayayyakin da ake amfani da su wajen samar da shi.

Shi kuwa shugaban ƙungiyar masu samarwa da sayar da taki ta Najeriya, Abubakar Kassim, ya bayyana cewa akwai albarkatun da za su iya samar da tan 148,000 na takin NPK cikin makonni masu zuwa, wanda zai kai buhuna kusan miliyan uku.

Ya ƙara da cewa akwai wasu tan 29,000 na taki da aka riga aka kammala haɗawa, waɗanda za a iya fara saye da rabawa nan take.

Kassim ya ce masana'antun ƙasar na da ƙarfin samar da buhunan taki kusan miliyan uku da rabi a cikin lokacin da aka tsara.

Gwamnatin tarayya ta kuma amince da Bankin Noma na Najeriya da Bankin Masana'antu su kula da harkokin kuɗaɗen gudanar da shirin.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse • 99.5 FM