NLC da TUC sun samu saɓani kan tallafin 70,000 na ma'aikata

Manyan ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya, NLC da TUC sun samu saɓani kan tallafin sufuri na naira 70, da gwamnatin ƙasar za ta bai wa ma'aikatan ƙasar tsawon wata shida.
A makon da ya gabata ne wakilan NLC da na gwamnatin tarayya suka cimma wata yarjejeniya da ta ƙunshi bai wa ma'aikatan ƙasar tallafin sufuri na naira 70,000 a kowane wata har tsawon wata shida.
To sai kwanaki bayan hakan ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta nuna rashin amincewa da matakin, tana mai watsi da shi.
Cikin wata sanarwar da shugaba da sakataren ƙungiyar na ƙasa, festus Osifo da Nuhu Toro suka sanya wa hannu, TUC ta ce gwamnatin tarayya na da damar da za ta iya ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 300,000 maimakon 70,000.
To sai dai cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels, shugaban ƙungiyar NLC, Joe Ajaero ya ce ƙungiyarsa na da ikon yin shawarwari ita kaɗai kan batutuwan da suka shafi ƙwadago, bisa ƙa’idar Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya (ILO).
Ya ƙara da cewa saɓanin haka ƙungiyar TUC ba za ta iya cimma yarjejeniya da gwamnati ita kaɗai ba, dole sai da NLC.



