Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Jigawa ta Gwangwaje NDLEA reshin jihar da sabuwar mota Hilux domin ƙarfafa yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.

Usman Muhammad Ismail 2 views
Gwamnatin Jigawa ta Gwangwaje NDLEA reshin jihar da sabuwar mota Hilux  domin ƙarfafa yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.

Gwamnatin jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar A. Namadi ta bai wa hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA reshen jihar kyautar sabuwar motar aiki ƙirar Toyota Hilux 2025 domin ƙara ƙarfafa ayyukan hukumar wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da fataucinsu.

Wannan mataki na nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro wajen kare al'umma, musamman matasa, daga illolin miyagun ƙwayoyi.

Da yake bayyana farin cikinsa kan wannan tallafi Kwamandan NDLEA na jihar Jigawa, Hassan Katangana Kabaju ya nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa wannan kyakkyawar gudummawa. Ya kuma bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta ba dare ba rana domin yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.

A cewar mai magana da yawun rundunar, Hassan Habibullah.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse • 99.5 FM