Freedom Radio Dutse
Muryar Jama'a, Dutse
Yanzu-yanzu
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin DauraGwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura
← Labarai
Masarauta

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura

Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da dukkan ayyukan hukuma da tafiye-tafiyen Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, sakamakon zargin cin zarafin wata mata ‘yar ƙasar waje da ake dangantawa da shi.

Gwamnatin ta kuma kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike kan zargin da ya yaɗu a kafafen sada zumunta.

Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar, Bala Salisu Zango, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta ce Gwamna Dikko Umaru Radda ya nuna matuƙar damuwa kan zargin, tare da bayar da umarnin kafa kwamitin da zai binciki lamarin tare da ba gwamnati shawarwari.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa za ta aiwatar da sakamakon binciken da shawarwarin kwamitin domin tabbatar da an yi adalci.

Ta kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankulansu, su kasance masu bin doka da oda tare da ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

Freedom Radio Dutse 99.5 FM
Freedom Radio Dutse 99.5 FM · Kai tsaye
Live