SARKIN DUTSE YA BUKACI JAMI’AR GWAMNATIN TARAYYA DA KE DUTSE FUD TA ƘARA SABABIN KWASA-KWASAI

Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Dr. Muhammad Hamim Nuhu Sunusi CFR, ya bukaci Hukumar Gudanarwar Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse da ta buɗe wasu sabbin kwasa-kwasai da za su dace da buƙatun al’umma da kuma gudanar da bincike mai zurfi.
Mai Martaba Sarkin ya ce buɗe irin waɗannan kwasa-kwasai zai taimaka wajen samar da ilimin dogaro da kai, bunƙasa bincike da samar da ƙwararrun ma’aikata da za su taimaka wajen ci gaban al’umma da jihar baki ɗaya.
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi bakuncin Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Farfesa Ahmad Mohammed Gumel, a fadarsa.
Mai Martaba ya kuma jaddada muhimmancin da jami’o’i ke da shi wajen samar da ilimi mai amfani da kuma nemo hanyoyin magance matsalolin da al’umma ke fuskanta.


