Sarkin Dutse Ya Yi Kira Ga Mawadata Dasu Fitar da Zakka Domin Tallafa wa Mabukata

Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Dr. Muhammad Hamim Nuhu Sunusi CFR, ya yi kira ga duk waɗanda Allah Ya azurta da su himmatu wajen fitar da haƙƙin Allah na zakka domin mabukata su amfana da ita.
Mai Martaba Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen rabon zakkar Gundumar Aujara da aka gudanar a Masarautar Dutse.
Sarkin ya yaba da irin ƙoƙarin da Sarkin Sudan, Alhaji Shaaibu Maigida, da kuma Sarkin Shanun Dutse, wanda kuma shi ne Kwamishinan Ayyuka na Jihar Jigawa, Alhaji Gambo S. Malam, ke yi na ci gaba da fitar da zakka a duk shekara domin tallafa wa masu buƙata.
Haka kuma, Mai Martaba ya yi kira ga al'umma da su ci gaba da zaman lafiya da juna, tare da gujewa ɗaukar doka a hannu, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai da zaman lafiya wajen cigaban al'umma.
