Koma Labarai
Masarauta

babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai ɗorewa ba tare da dogaro da sana’o’i da ƙirƙire-ƙirƙire ba

Usman Muhammad Ismail 0 views
babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai ɗorewa ba tare da dogaro da sana’o’i da ƙirƙire-ƙirƙire ba

Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Nuhu Muhammad Sanusi, ya bayyana cewa babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai ɗorewa ba tare da dogaro da sana’o’i da ƙirƙire-ƙirƙire ba, musamman a wannan lokaci da duniya ke karkata sosai kan fasaha da kirkire-kirkire.

Sarkin Dutse ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kammala zagayen wasu sassa na birnin Dutse, inda ya duba tare da yaba da ayyukan raya birni da ci gaban da gwamnatin Jihar Jigawa, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi, ke aiwatarwa.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM