Koma Labarai
Labarai

Mai dakin shugaban kasa Senata Remi tace bata roko, don haka matasan Najeriya su koyi wadatar zuci, da juriya, da aiki tukuru.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Mai dakin shugaban kasa Senata Remi tace bata roko, don haka matasan Najeriya su koyi wadatar zuci, da juriya, da aiki tukuru.

Uwar gidan shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu Senata Oluremi Tinubu tace bata roko face dai yin aiki da abin da Allah ya bata.

A sabo da haka nema ta shawarci matasan kasar nan dasu kasance masu wadatar zuci da juriya da kuma yin aiki tukuru.

Senata Oluremi ta bayyana haka ne lokacin da ta karbi bakuncin shugabannin matasan jamiyar APC a Abuja wadda ta basu sabuwar Mota fil.

Tana mai cewa a wannan matsayin da nake bana rokon kowa komai duk abin da Allah ya bani da shi nake aiki don haka ina mai yi muku wa'azi ku koyi wadatar zuci karku zama masu roke-roke.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM