Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA, reshen Jihar Jigawa, ta gana da shugabannin manyan makarantun gaba da sakandare na jihar domin tsara yadda za a fara aiwatar da Manufar Gwajin kan Amfani da Miyagun Kwayoyi — Drug Integrity Test Policy ga sabbin dalibai da wadanda ke ci gaba da karatu.

Taron ya gudana ne a Nuhu Sunusi Hall/Auditorium na Jami’ar Tarayya da ke Dutse, karkashin jagorancin Kwamandan NDLEA na jihar Jigawa, CN Hassan Katangana Kabaju.
Manufar taron ita ce hada kai tsakanin NDLEA da shugabannin makarantun gaba da sakandare, da daidaita hanyoyin gudanar da gwajin, tare da samar da tsarin da zai ba da damar aiwatar da manufar cikin sauki da lokaci guda a dukkan manyan makarantun jihar.
Da yake jawabi a wajen taron, Kwamanda Kabaju ya bayyana cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke barazana ga karatun dalibai, tsaron makarantu da kuma makomar matasa.
Ya jaddada cewa manufar gwajin ba wai don farautar dalibai ko hukunta wadanda ba su da laifi ba ce, illa dai wata hanya ce ta rigakafi, gano matsala tun da wuri da kuma samar da taimako ga daliban da suke bukata.
A cewarsa, manufar ita ce kare daliban da ba sa amfani da miyagun kwayoyi, tare da gano wadanda suke bukatar shawara, jinya ko sauran hanyoyin tallafi, domin tabbatar da cewa makarantun gaba da sakandare sun kasance wuraren samun ingantaccen ilimi da tsaro.
A yayin taron, NDLEA ta gabatar da cikakken tsarin aiwatar da gwajin, wanda ya kunshi yadda za a gudanar da gwajin, sirrin bayanan dalibai, yadda za a kula da samfurorin gwaji, ba da shawarwari, jinya da kuma tura daliban da sakamakon gwajinsu ya nuna suna bukatar taimako zuwa cibiyoyin da suka dace.
Shugabannin makarantun da suka halarci taron sun kuma gabatar da tambayoyi da damuwarsu kan batutuwan da suka shafi kayan aiki, kudade da kuma tsarin tallafawa daliban da za a samu sakamakon gwajinsu.
Bayan tattaunawa, mahalarta taron sun cimma matsaya kan samar da tsari guda daya da za a yi amfani da shi wajen aiwatar da manufar a dukkan manyan makarantun jihar.
Taron ya samu wakilcin dukkan manyan makarantun gaba da sakandare da aka gayyata daga sassan Jihar Jigawa.Daga cikin wadanda suka halarta akwai wakilan Federal University of Technology, Babura; Federal University Dutse; College of Islamic and Legal Studies, Ringim; College of Education, Gumel; College of Health Technology, Hadejia; College of Nursing Sciences, Hadejia; Jigawa State Polytechnic, Dutse; Kazaure College of Nursing Sciences; Iqraa College of Nursing; National Teachers Institute, da kuma National Open University of Nigeria, Dutse Study Centre, da sauran cibiyoyin ilimi.
Haka kuma, an samu halartar wakilan Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, kungiyar daliban Jihar Jigawa ta kasa da kuma wakilin Mai Martaba Sarkin Dutse.
Hukumomin tsaro da suka halarci taron sun hada da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, DSS, FRSC, Immigration, NSCDC, Federal Fire Service, Customs da kuma Nigeria Forest Security Service.A karshen taron, shugabannin manyan makarantun sun amince da manufar Drug Integrity Test Policy, tare da daukar matakai da suka hada da:
Na farko, nada jami’an da za su zama masu kula da wannan shiri a kowace makaranta, wadanda za su rika hulda da NDLEA.
Na biyu, fara wayar da kan dalibai, iyaye da ma’aikatan makarantu kan manufar gwajin.
Na uku, hada gwajin cikin tsarin shigar da sabbin dalibai da kuma rajistar wadanda ke ci gaba da karatu.
Na hudu, samar da sassan ba da shawarwari da tura dalibai zuwa wuraren jinya ko taimako, tare da hadin gwiwar NDLEA.
A jawabinsa na rufe taron, Kwamandan NDLEA na Jigawa, CN Hassan Katangana Kabaju, ya gode wa shugabannin makarantun da sauran masu ruwa da tsaki bisa hadin kan da suka nuna.
Ya kuma bukaci kowa da ya dauki wannan shiri a matsayin nauyin hadin gwiwa wajen kare matasan Jigawa daga illar shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Ya bayyana cewa Jigawa ta kafa wani muhimmin mataki wajen kare cibiyoyin ilimi daga matsalar miyagun kwayoyi, yana mai cewa burin NDLEA shi ne ganin manyan makarantun jihar sun zama cibiyoyin kwarewa da ingantaccen ilimi, ba wuraren yaduwar shaye-shayen miyagun kwayoyi ba.
ACN Abdullahi Wada LLB, MPPA, ASIOARM, CPM, MCIHRM, VISO, CPSC
A madadin Kwamandan NDLEA, Jihar Jigawa.



