Koma Labarai
Siyasa

Ministan Abuja Nyeson Wike yace Tinubu zai lashe zaben 2027 cikin sauki fiye da na 2023

Usman Muhammad Ismail 0 views
Ministan Abuja Nyeson Wike yace Tinubu zai lashe zaben 2027 cikin sauki fiye da na 2023

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai fi samun sauƙin lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, idan aka kwatanta da zaɓen shekarar 2023.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin da yake duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a wasu sassan Babban Birnin tarayya, Abuja.

Ministan ya ce rarrabuwar kawuna da ake samu a tsakanin jam’iyyun adawa za ta sa ya yi musu wahala wajen haɗa ƙarfi da kuma fuskantar Tinubu da gagarumin ƙalubale a zaɓen 2027.

Tsohon gwamnan jihar Rivers ya ƙara da cewa jam’iyyun adawa sun yi rauni sakamakon sauya sheƙa da kuma wasu sauye-sauyen siyasa da ake samu gabanin zaɓen shekarar 2027.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM