Koma Labarai
Siyasa

Alhaji Atiku Abubakar ya ce ba zai sake tsayawa takara ba idan ya Sha kaye a zaben 2027.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Alhaji Atiku Abubakar ya ce ba zai sake tsayawa takara ba idan ya Sha kaye a zaben 2027.

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce ba zai sake neman takarar shugaban ƙasa ba idan har ya sha kaye a zaɓen shekarar 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi cikin harshen Hausa, inda ya ce tuni ya yanke shawarar cewa zaɓen 2027 zai kasance na ƙarshe da zai shiga takarar shugabancin ƙasar.

Ya kuma buƙaci masu kaɗa ƙuri’a da su zauna a rumfunan zaɓe har zuwa lokacin da aka ƙirga ƙuri’u, domin tabbatar da cewa an ƙirga ƙuri’arsu kuma an kare zaɓin da suka yi.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM