Koma Labarai
Siyasa

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya ce ba zai bari 'yan adawa su kai shi kasa ba, har sai an fafata a zaben 2027 tun da INEC ba goyon bayan kowa take yi ba.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya ce ba zai bari 'yan adawa su kai shi kasa ba, har sai an fafata a zaben 2027 tun da INEC ba goyon bayan kowa take yi ba.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce hukumar zaben kasar mai zaman kanta ce, don haka ba zai bari jam'iyyun adawa su rinjaye shi ko su hana shi ci gaba da fafatawa ba.

Yayin da yake karbar bakuncin kungiyar limaman cocin katolika ta Najeriya (CBCN) , Tinubu ya ce wadanda ke zargin INEC da son kai, kame-kame kawai suke yi. Har ila yau, shugaban ya ce yana sane da cewa akwai masu kokarin kwace masa mulki, amma ya jaddada cewa zai ci gaba da fafatawa har zuwa karshen takara.

Shin kuna ganin INEC za ta gudanar da zaben 2027 cikin gaskiya da adalci?

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM