Koma Labarai
Siyasa

Remi Tinubu ta ce za ta rika sanya kayan gargajiya na Akwete idan Tinubu ya sake lashe zabe

Usman Muhammad Ismail 0 views
Remi Tinubu ta ce za ta rika sanya kayan gargajiya na Akwete idan Tinubu ya sake lashe zabe

Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa za ta riƙa sanya kayan gargajiyar Akwete idan mijinta, shugaba Bola Tinubu, ya sake lashe zaɓen wa'adi na biyu.

Ta bayyana hakan ne yayin ziyararta ta farko ƙauyen masu saƙar Akwete da ke Ƙaramar hukumar Ukwa ta Gabas a jihar Abia, inda ta sanar da bayar da tallafin naira biliyan biyu domin farfaɗo da masana'antar saƙar Akwete.

Remi Tinubu ta ce kayan Akwete suna da muhimmanci saboda suna wakiltar al'adun Najeriya, tare da yabawa mata masu wannan sana'a bisa kokarin da suke yi na gadar da ita zuwa tsararraki masu zuwa.

Ta kuma buƙaci 'yan Najeriya su riƙa amfani da kayayyakin da ake samarwa a cikin gida domin tallafa wa sana'o'in gargajiya da samar da ayyukan yi.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM