Koma Labarai
Labarai

Jigawa ta kara kaimi kan yaki da miyagun kwayoyi, yayin da NDLEA ta bayyana kama mutum 77,859 tare da kwace kilo miliyan 14.8 na miyagun kwayoyi cikin shekara biyar

Usman muhammad Ismail 0 views
Jigawa ta kara kaimi kan yaki da miyagun kwayoyi, yayin da NDLEA ta bayyana kama mutum 77,859 tare da kwace kilo miliyan 14.8 na miyagun kwayoyi cikin shekara biyar

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA), Brig.-Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya), ya ce hukumar ta kama mutane 77,859 tare da ƙwace sama da kilo miliyan 14.8 na miyagun ƙwayoyi tsakanin 2021 da 2025.

Marwa ya bayyana haka ne a birnin Dutse yayin bikin sanya hannu kan dokokin zartarwa da gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yi domin ƙarfafa yaƙi da shaye-shaye. Ya ce an yanke wa mutum 14,122 hukunci, yayin da sama da mutum 50,000 suka amfana da shawarwari da jinya a cibiyoyin gyaran masu shaye-shaye na NDLEA.

Ya kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa kan matakan da take ɗauka wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi, yayin da gwamna Namadi ya ce sabbin dokokin na da nufin kare makomar matasa da rage matsalar shaye-shaye a jihar.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM