Koma Labarai
Labarai

Shugaban NDLEA ya bukaci a fara yin gwajin Kwaya ga masu Shirin yin Aure kamar yadda ake yin na HIV da Sikila kafin daura Aure.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Shugaban NDLEA ya bukaci a fara yin gwajin Kwaya ga masu Shirin yin Aure kamar yadda ake yin na HIV da Sikila kafin daura Aure.

Shugaban hukumar yaki da Sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa NDLEA ya bukaci a fara yiwa masu shirin yin Aure gwajin Kwaya kamar yadda ake yin na HIV da Sikila.

Marya ya bayyana haka ne a Gidan gwamnatin jihar Jigawa dake Dutse, Jim kadan bayan gwamna Malam Umar Namadi ya sanya hanu kan dokar wayar da kan matasa illar ta'ammali da kayan maye da kuma canza dabi'un mutane.

A cewar shugaban matakin gwajin zai taimaka wajen dakile Aurar da yara mata ga masu ta'ammali da kayan maye.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM