Kungiyar 'Yan Jarida ta kasa (NUJ) ta tabbatar Aminu Umar Shuwajo a matsayin sakataran kungiyar na jihar Jigawa kana mamba a majalisar Koli ta Kungiyar (NEC)

Kungiyar 'yan Jarida ta kasa ta kaddamar da Comerade Aminu Umar Shuwajo a matsayin cikakken sakataran kungiyar reshen jihar Jigawa kana mamba a majalisar kolin kungiyar, bayan shafe tsawon lokaci yana rikon kwaryar matsayin.
A jiya ne dai shugaban kungiyar na kasa Comrade Alhassan Yahya Abdullahi ya kaddamar da Comerade Shuwajo kan wannan matsayi a matsayin sabon mambobin majalisar kolin kungiyar tare da Hauwa S Zaharaddin daga jihar Kano a matsayin sakatariyar kungiyar reshen jihar Kano kuma mamba a majalisar Koli, bayan ta rikon kwaryar matsayin na wani lokaci.
Dukkanin sabin sakatarorin guda biyu sun samu sabon matsayin ne, biyo bayan ajiye matsayin sakataran kungiyar reshen jihar Jigawa da Aisha Abba Ahmad ta yi bisa radin kanta, ya yin da ita ma Hauwa S Zahraddeen ta zama sakatariyar kungiyar reshen jihar Kano bayan sauke asalin sakataran dake kai.
Comerade Aminu Umar Shuwajo wadda ma'aikacin Freedom Radio ne reporter kuma producer ya kasance tsohon shugaban 'kungiyar reshen Freedom Radio Dutse kafin a a zabe shi a matsayin mataimakin sakataran kungiyar na jiha cikin watan mayun shekarar 2025.



