SARKIN DUTSE YA BUKACI NUJ TA ƘARFAFA ƘOƘARIN MAGANCE MATSALAR ’YAN JARIDUN BOGI

Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Dr. Muhd Hamim Nuhu Sunusi CFR, ya buƙaci Ƙungiyar ’Yan Jaridu ta Ƙasa, NUJ, da ta bullo da wani tsari na musamman da zai taimaka wajen magance matsalar ’yan jaridun bogi da kuma yaɗa labaran ƙanzon kurege a cikin al’umma
Mai Martaba Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jaridu ta Ƙasa, Comrade Alhassan Yahaya Abdull, ya kai masa ziyarar girmamawa a fadarsa da ke Dutse.
Sarkin ya bayyana cewa yaɗa labaran ƙarya na iya haifar da rudani, ɓata suna da kuma kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
Ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da cewa aikin jarida yana gudana bisa ƙa'idojin sana'a, gaskiya da riƙon amana, yana mai kira ga ƙungiyar da ta ƙara ƙoƙari wajen tantance masu ikirarin aikin jarida tare da wayar da kan jama'a kan illolin labaran ƙarya.
A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jaridu ta Ƙasa, Comrade Alhassan Yahaya Abdull, ya bayyana godiyarsa ga Mai Martaba Sarkin Dutse bisa karɓar tawagar da kuma shawarwarin da ya bayar.
Ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin kare martabar aikin jarida da tabbatar da cewa jama'a na samun sahihan bayanai daga ƙwararrun ’yan jarida.



