Koma Labarai
Labarai

Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, ta kori dalibai 11 daga makaranta bayan an same su da laifin satar jarabawa.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, ta kori dalibai 11 daga makaranta bayan an same su da laifin satar jarabawa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama'a na jami'ar, Abdullahi Yahaya Bello, ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce Majalisar Dattawan jami'ar, a zamanta na 76 da ta gudanar a ranar 30 ga Yuli, 2026, ta amince da rahoto na 18 na Kwamitin Jarabawa da Laifukan da suka shafi gudanar da jarabawa.

Baya ga korar dalibai 11, jami'ar ta kuma dakatar da wasu dalibai 23 na tsawon zangon karatu biyu.

Haka kuma, an bai wa dalibai uku takardar gargadi, yayin da aka wanke dalibi guda daya daga zargin da ake masa.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM