Tinubu ya umarci EFCC ta buɗe asusun gwamnatin jihar Osun cikin gaggawa

Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci hukumar EFCC da ta gaggauta komawa kotu domin neman a soke umarnin da ya ba ta damar rufe asusun gwamnatin jihar Osun.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Tinubu ya ce matakin da EFCC ta ɗauka ya ba shi kunya saboda "lokacin da ta ɗauki matakin."
"Dole ne in bayyana cewa abin ya ba ni kunya ƙwarai. Ba wai saboda EFCC ta aiwatar da aikinta ba ne duk da cewa ta samu umarnin kotu ba, sai dai saboda lokacin da ta ɗauki wannan mataki," in ji shugaban.
Ya ce duk wani mataki da hukumomin gwamnatin tarayya suka ɗauka, ana danganta shi da shugaban ƙasa ne ko da kuwa ba shi da masaniya kan abin da aka aiwatar.
Shugaban ya kuma jaddada cewa tun lokacin da ya hau mulki ya guji tsoma baki cikin ayyukan EFCC da sauran hukumomin bincike domin ba su damar gudanar da aikinsu cikin 'yanci.
"Na kasance ina jaddada cewa dole ne a bar hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran hukumomin tabbatar da doka su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa, ba tare da tsoro, son rai ko katsalandan na siyasa ba."
Sai dai Tinubu ya ce, duk da cewa har yanzu bai samu cikakken bayani kan dalilan da suka sa EFCC ta nemi kotu ta ba ta umarnin rufe da asusun gwamnatin jihar Osun ba, yana ganin lokacin da aka ɗauki matakin bai dace ba.
"Jihar Osun na daf da gudanar da zaɓen gwamna. Don haka bai kamata a yi wani abu da zai sa a yi zargin cewa ana amfani da EFCC ko wata hukumar gwamnatin tarayya wajen yin katsalandan a zaɓen ba."
Saboda haka shugaban ya ce ya ba hukumar umarni ta ɗauki matakin gaggawa.
"Na umarci EFCC da ta gaggauta komawa kotu domin neman a soke wannan umarni, tare da dakatar da duk wani mataki da ta ɗauka kan gwamnatin jihar Osun dangane da wannan lamari."
EFCC ta samu umarnin kotu a ranar 5 ga Agustan 2026 na rufe asusun gwamnatin jihar Osun. Sai dai zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, hukumar ba ta fitar da karin bayani kan dalilan da suka sa ta nemi umarnin kotun ba.



