Koma Labarai
Ilimi

Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Dr. Muhammadu Hamim Nuhu Sunusi CFR, ya bukaci Gwamnatin Jihar Jigawa da ta bibiyi tare da aiwatar da dokar da ta tilasta wa iyaye tura ’ya’yansu makaranta.

Usman Muhammad Ismail 1 views
Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Dr. Muhammadu Hamim Nuhu Sunusi CFR, ya bukaci Gwamnatin Jihar Jigawa da ta bibiyi tare da aiwatar da dokar da ta tilasta wa iyaye tura ’ya’yansu makaranta.

Mai Martaba Sarkin ya ce aiwatar da irin wannan doka na daga cikin matakan da za su taimaka wajen magance matsalar rashin zuwa makaranta da wasu yara ke fuskanta a jihar.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi bakuncin tawagar Kwamitin Maida Yara Makaranta, karkashin jagorancin Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta Jihar Jigawa, Garba Dalladi Muhammad, a fadarsa da ke Dutse.

Mai Martaba ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwar iyaye, malamai, sarakuna da gwamnati wajen tabbatar da cewa yara sun samu damar zuwa makaranta domin samun ilimi mai inganci.

A wani ɓangaren kuma, Mai Martaba Sarkin Dutse ya yabawa Malam Sani Maje, shugaban Sabil Academy, bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen raya harkokin addinin Musulunci da ilimi a jihar Jigawa.

Sarkin ya bayyana ayyukan Malam Sani Maje a matsayin gudunmawa mai muhimmanci wajen tarbiyyantar da matasa da ƙarfafa sha’anin ilimi da addini a jihar

Ready to PlayFreedom Radio Dutse • 99.5 FM