Gwamnatin Jihar Jigawa ta tura ɗalibai 65 zuwa jami'a a ƙasar China domin ƙara ilimi da ƙwarewa a fannin noma, wanda kusan kashi 90% na al'ummar jihar ke dogaro da shi.
Usman Muhammad Ismail 1 views

Da yake jawabi lokacin da yake bankawana da daliban a gidan gwamnatin jihar Jigawa dake Dutse gwamna Malam Umar Namadi, ya bayyana daukar nauyin karatun daliban a matsayin guda cikin kudirorin gwamnatinsa 12.



