Koma Labarai
Ilimi

TAWAGAR JIHAR JIGAWA TA KAI ZIYARCI JAMI'AR ISLAMIC UNIVERSITY IN UGANDA DOMIN ƘARFAFA HAƊIN GWIWAR ILIMI

Usman Muhammad Ismail 0 views
TAWAGAR JIHAR JIGAWA TA KAI ZIYARCI JAMI'AR ISLAMIC UNIVERSITY IN UGANDA DOMIN ƘARFAFA HAƊIN GWIWAR ILIMI

A wani muhimmin yunƙuri na ƙara bunƙasa harkokin ilimi da samar da sabbin damammaki ga ɗalibai da gwamnatin jihar Jigawa take, Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Kimiyya da Fasaha ta Jihar Jigawa, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ya jagoranci wata tawaga ta musamman zuwa Jami'ar Islamic University in Uganda (IUIU) da ke ƙasar Uganda domin gudanar da ziyarar aiki tare da tattaunawa kan hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwar ilimi.

A yayin ziyarar, tawagar ta gana da Shugaban Jami'ar (Vice Chancellor/Rector) na Islamic University in Uganda (IUIU), Professor Isma’il Simbwa Gyagyenda, tare da manyan jami’an jami’ar. Domin tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka shafi haɗin gwiwar ilimi, da samar da sabbin damammaki ga ɗalibai da matasa.

Ziyarar ta kuma ba tawagar damar fahimtar wasu daga cikin tsare-tsare da dabarun da Jami’ar Islamic University in Uganda ke amfani da su wajen haɓaka ingancin ilimi, ƙarfafa ƙwarewar ɗalibai, da samar da ilimi mai dacewa da buƙatun zamani.

Wannan ziyara na ƙara jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyin ilimi na cikin gida da na ƙasa da ƙasa, musamman bunƙasa bincike, da samar da damammaki masu ɗorewa ga matasa.

A ƙarshe, ziyarar ta kasance wata muhimmiyar dama ta ƙarfafa fahimtar juna da buɗe ƙofofin sabbin hanyoyin haɗin gwiwa tsakanin Jihar Jigawa da Islamic University in Uganda, domin ci gaba da gina ingantaccen tsarin ilimi mai amfanar al’umma da kuma dacewa da ƙalubalen ƙarni na 21.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM