GWAMNAN JIHAR JIGAWA YA NAƊA FARFESA ISA YUSUF CHAMO SHUGABAN KWAMITIN GASAR KARATUN ALƘUR’ANI TA ƘASA KARO NA 41

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar A. Namadi, ya naɗa Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Kimiyya da Fasaha, Farfesa Isa Yusuf Chamo, a matsayin Shugaban Kwamitin Shirye-shiryen gudanar da Gasar Karatun Alƙur’ani ta Ƙasa karo na 41 (41st National Qur’anic Recitation Competition), wadda za a gudanar a Jihar Jigawa a watan Nuwamba 2026.
Gwamna Namadi ya ƙaddamar da kwamiti mai mutum 38 domin jagorantar shirye-shiryen gasar da tabbatar da gudanar da ita cikin tsari, inganci da martaba.
An kuma naɗa Dakta Lawan Yunusa Dan Zomo, Kwamishinan Ilimi na matakin farko, a matsayin Mataimakin Shugaban Kwamitin na Farko, yayin da Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, zai kasance Mataimakin Shugaban Kwamitin na Biyu. Malam Adamu Ibrahim, Daraktan Kuɗi da Mulki na Hukumar Kula da Ilimin Musulunci da Bunƙasa Harshen Larabci ta Jihar Jigawa, shi ne Sakataren Kwamitin.
Kwamitin ya ƙunshi kwamishinoni, masu ba Gwamna shawara da wakilan manyan sarakunan gargajiya guda biyar na Jihar Jigawa.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da kwamitin a Gidan Gwamnati da ke Dutse, Gwamna Namadi ya bayyana cewa an zaɓi mambobin ne bisa ƙwarewa, cancanta da kwarewar gudanar da ayyuka, domin tabbatar da nasarar wannan gagarumar gasar.
Ya ce kwamitin zai kula da dukkan shirye-shiryen gasar, ciki har da samar da kuɗaɗen gudanar da ita ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati, ƙananan hukumomi, kamfanoni da daidaikun mutane daga ciki da wajen Jihar Jigawa.
Haka kuma, kwamitin zai tabbatar da samar da kyaututtuka masu kyau ga waɗanda suka yi nasara, da kuma kula da jin daɗin mahalarta da sauran muhimman abubuwan da za su tabbatar da gudanar da gasar cikin nasara.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ya gode wa Gwamnan bisa wannan dama, tare da tabbatar da cewa zai haɗa kai da sauran mambobin kwamitin domin ganin an gudanar da gasar karo na 41 cikin nasara da martaba.



