Koma Labarai
Labarai

Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta yi karatun na biyu kan ƙarin kasafin kuɗi naira biliyan 46 da Gwamnan jihar, Malam Umar Namadi, ya aikewa Majalisar a jiya Laraba.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta yi karatun na biyu kan ƙarin kasafin kuɗi naira biliyan 46 da Gwamnan jihar, Malam Umar Namadi, ya aikewa Majalisar a jiya Laraba.

Kakakin Majalisar Dokokin jihar Jigawa, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin, ne ya tabbatar da hakan jim kaɗan bayan Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Honarabul Lawan Muhammad Dansure, ya jagoranci mahawara kan kudirin.

Bayan kammala mahawarar, Majalisar ta tura kudirin zuwa Kwamitin Kasafin Kuɗi domin yin nazari tare da gabatar da rahotonsa ga Majalisar nan da ranar Laraba mai zuwa.

A yayin zaman, Majalisar ta kuma dage zamanta zuwa ranar Alhamis na mako mai zuwa, domin ci gaba da ayyukanta.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse • 99.5 FM