Yan Sandan Jigawa Sun Cafke Mutane Uku da Ake Zargi da Safarar Miyagun Ƙwayoyi,

Rundunar 'Yan Sandan jihar Jigawa ta sanar da samun gagarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da kuma kare lafiyar al'umma, bayan da ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a hare-haren da jami'anta suka kai bisa sahihan bayanan sirri a sassa daban-daban na jihar.
Wadanda aka kama sun haɗa da Umar Rabiu (Sarka) mai shekaru 22 daga Unguwar Gamji, Auwalu Muhammad mai shekaru 25 daga Gusau Quarters, da kuma Umar Akilu mai shekaru 25 daga ƙauyen Kuka.
A cewar rundunar, samamen wani ɓangare ne na ci gaba da yaƙin da take yi da masu sayarwa, rabawa da amfani da miyagun ƙwayoyi. A yayin samamen, jami'an sun kwato jimillar ƙwayoyi 5,676 na miyagun ƙwayoyi daban-daban da ake zargin haramtattu ne.
Kayan da aka kwato sun haɗa da:
Ƙwayoyin Exol guda 3,833.
Tramadol guda 204.
Diazepam guda 919.
Pregabalin guda 114.
Rubber Solution guda 101.
Lara Capsules guda 30.
Kwalaben Codeine Syrup.
Lita biyu na abin da ake kira "Suck and Die".
Da kuma busassun ganyen da ake zargin wiwi ne (Cannabis sativa) guda ɗaya tare da ƙananan kunshe-kunshe 475.
Haka kuma, jami'an sun kwato kuɗi har Naira 93,626, waɗanda ake kyautata zaton kuɗaɗen da aka samu ne daga harkar safarar miyagun ƙwayoyi.
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Jigawa ya yabawa jami'an da suka gudanar da aikin bisa ƙwarewa, jajircewa da ƙwazo. Ya ce safara da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa aikata laifuka da lalacewar tarbiyya, musamman a tsakanin matasa.
Ya kuma gargaɗi masu safara, sayarwa ko amfani da miyagun ƙwayoyi da su daina, domin rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri da samame domin tarwatsa cibiyoyin masu aikata irin waɗannan laifuka tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Rundunar ta tabbatar da cewa an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa tanadin doka.



