Koma Labarai
Labarai

Tinubu ya amince da karin albashin Sojoji da kashi 30 zuwa 80

Usman Muhammad Ismail 0 views
Tinubu ya amince da karin albashin Sojoji da kashi 30 zuwa 80

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin albashin jami’an rundunar sojin Najeriya da zai kai tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin 100, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumban 2026.

Sanarwar da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai , Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata ta ce karin albashin zai shafi sojoji kusan 250,000 a fadin kasar.

A sabon tsarin, manyan hafsoshi daga mukamin Kanal zuwa sama za su samu karin kashi 30, yayin da jami’ai daga Kanal zuwa Warrant Officer za su samu karin kashi 50. Sojoji daga mukamin Private zuwa Staff Sergeant kuwa za su samu karin kashi 80 cikin 100.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa matakin na daga cikin kokarin gwamnatin sa na inganta jin dadin sojoji da kuma nuna godiya ga sadaukarwar da suke yi wajen yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a Najeriya. Ya kuma jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da samar wa rundunar soji kayan aiki da fasahar zamani domin inganta ayyukansu.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM