'Yansanda a Katsina sun kama mutumin da ake zargin ya kashe 'yarsa don taki amincewa da mijin da ya zaba mata.
Usman Muhammad Ismail 0 views

Rundunar ƴan sandan ta bayyana mutumin a matsayin Kabir Sani mazaunin unguwar rukunin gidajen 'Shagari Low-Cost'.
Ƴan sandan sun ce maƙotan Kabir sun tabbatar da cewar tun daren Laraba har zuwa wayewar garin Alhamis Kabir ke lakaɗawa ƴarsa Ummulkhairi duka a kan sai ta amince da zaɓin da ya mata amma taƙi.
Rahotanni sun ce abokan ta ne su ka tarar da gawar ta da safe lokacin da suka biya mata su tafi makaranta, abinda ya suka shaidawa ƴan sanda.



