Koma Labarai
Labarai

Ni ban ce idan na dawo da tallafin man fetur zan cire shi daga baya ba - Atiku

Usman Muhammad Ismail 0 views
Ni ban ce idan na dawo da tallafin man fetur zan cire shi daga baya ba - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce shirin da yake da shi na tallafawa harkar man fetur ba wai komawa tsarin tallafin man fetur na shigo da shi daga ƙasashen waje ba ne, sai dai tallafi ne da za a mayar da hankali wajen ƙara samar da man fetur a cikin gida da rage tsadar rayuwa.

Atiku ya bayyana hakan ne ta hannun babban mataimakinsa na musamman kan yaɗa labarai, Phrank Shaibu, a wata sanarwa da aka fitar ranar Talata.

Shaibu ya ce bayanin ya zama dole ne bayan wasu kalaman da aka danganta ga Paul Ibe, wanda ya ce gwamnatin Atiku za ta dawo da tallafin man fetur sannan ta cire shi daga baya.

Ya bayyana wannan magana a matsayin bayani da ba a ba da izini ba, wanda bai dace da manufar Atiku ba, yana mai cewa masu magana a madadin ɗan takarar ba su da ikon sauya ko ƙirƙirar wata manufa da ɗan takarar bai bayyana ba.

A cewar Shaibu, Atiku bai taɓa cewa za a dawo da tsarin tallafin man fetur na shigo da mai daga ƙasashen waje sannan a cire shi a wata ƙayyadaddiyar rana ba.

Ya ce abin da Atiku ke shirin yi shi ne samar da tallafi mai iyaka, wanda aka ware masa kasafin kuɗi a fili tare da sanya ido da binciken masu zaman kansu, domin tallafa wa matatun man fetur na cikin gida da bunƙasa samar da mai.

Shaibu ya ƙara da cewa ba za a sanya ranar da za a dakatar da tallafin ba kai tsaye ba, domin za a rage tallafin ne yayin da samar da man fetur a cikin gida ke ƙaruwa, wadatar mai ke daidaituwa, gasa a kasuwa ke ƙaruwa, sannan farashin mai ya fara sauƙi ba tare da dogaro da tallafin gwamnati ba.

Ya kwatanta manufar da ginin gida, inda ya ce ba a cire kayan tallafa wa gini saboda kalanda ta nuna lokaci ya yi, sai an cire su ne lokacin da ginin ya kai matsayin da zai iya tsayawa da kansa.

Shaibu ya ce bai kamata ’yan Najeriya su karkata hankalinsu kan muhawarar kalmomin “cire tallafi” ko “mayar da tallafi” ba, maimakon haka ya kamata a mayar da hankali kan yadda za a rage tsadar rayuwa.

Ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mayar da illolin sauye-sauyen tattalin arzikinta kan iyalan Najeriya, yana mai cewa Atiku zai mayar da hankali wajen rage kuɗin samar da kaya da sufuri, ƙarfafa matatun man fetur na cikin gida da kuma dawo da ƙarfin sayen ’yan Najeriya.

Shaibu ya ce zaɓin da ke gaban ’yan Najeriya ba wai tsakanin cire tallafi da mayar da tallafi ba ne, illa tsakanin “Najeriya mai tsada” da “Najeriya mai sauƙin rayuwa.”

Sanarwar ta kasance mai ɗauke da sa hannun Phrank Shaibu, babban mataimakin Musamman na Atiku Abubakar kan yaɗa labarai a ranar 25 ga Agusta, 2026.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM