Koma Labarai
Labarai

Tinubu ya kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na 2027 inda ya naɗa Abdul'aziz Yari a matsayin darakta-Janar

Usman Muhammad ismail 0 views
Tinubu ya kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na 2027 inda ya naɗa Abdul'aziz Yari a matsayin darakta-Janar

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen 2027.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata, Abdulaziz Yari, ne aka naɗa Darakta-Janar na kwamitin, yayin da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, zai kasance Sakatare.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar da safiyar Asabar, wadda mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai , Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, za su kasance Shugaban kwamitin da Mataimakin Shugaban Kwamitin na farko, bi da bi.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, an naɗa shi Mataimakin Shugaban Kwamitin na biyu.

Sakataren APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, da Hadiza Bala-Usman, an naɗa su Mataimakin Sakatare da Mataimakiyar Sakatare.

Tinubu zai yi aiki tare da wasu masu ba shi shawara da suka haɗa da Bisi Akande, Segun Osoba, Sanata Rochas Okorocha, Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Florence Ita-Giwa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, an naɗa su Mataimakan Darakta-Janar masu kula da yankunan Arewa da Kudu.

Za su yi aiki tare da Sanata Opeyemi Bamidele da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibril Barau.

Sanata Adams Oshiomhole zai kasance Mataimakin Darakta-Janar mai kula da wayar da kan masu zaɓe da tattara jama’a, yayin da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, zai kasance Mataimakin Darakta-Janar mai kula da harkokin gudanarwa.

James Faleke, wanda ya taka muhimmiyar rawa a yaƙin neman zaɓen APC na 2022/2023, ya dawo a matsayin Mataimakin Darakta-Janar mai kula da tsare-tsare, daidaita ayyuka da sa ido kan zaɓe.

Zai yi aiki tare da daraktocin shiyyoyi, ciki har da Sanata Olushola Adeyeye a Kudu maso Yamma, Dr Ngozi Olejeme a Kudu maso Kudu, Sanata Uche Ekwunife a Kudu maso Gabas, Muntaqha Rabe a Arewa maso Yamma, Ahmed Muhammed Ketso a Arewa ta Tsakiya da Sanata Sani Danladi a Arewa maso Gabas.

Stella Okotete, Abdullahi Garba Ramat da Audu Maikori an naɗa su sakatarorin sashen tsara harkokin zaɓe.

Muiz Banire, SAN, zai jagoranci sashen shari’a a matsayin Darakta, tare da Liman Hassan da Babatunde Ogala a matsayin mataimakansa.

Ministan yaɗa Labarai da wayar da kan Jama’a, Mohammed Idris, zai kasance Daraktan Gudanarwa na Sashen yaɗa labarai.

Zai yi aiki tare da Dele Alake, Bayo Onanuga da Lanre Issa-Onilu.

Tunde Rahman, Sunday Dare, Daniel Bwala da Felix Morka an naɗa su Mataimakan Daraktoci na Gudanarwa a wannan sashe.

Segun Dada, wanda ya riƙe irin wannan matsayi a lokacin yaƙin neman zaɓen 2022, zai dawo a matsayin Daraktan shafukan sada zumunta , yayin da Solomon Arowolo zai kasance Sakatare.

Kwamitin yaƙin neman zaɓen ya kuma naɗa masu magana da yawun kamfen guda biyar, ƙarƙashin jagorancin Dele Alake, tare da Alwan Hassan, Ayobami Oyalowo, Kemi Asekun-Shittu da Adamu Fanda.

A cikin sanarwar, Shugaba Tinubu ya buƙaci dukkan mambobin kwamitin da su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar APC a zaɓen 2027.

Ya kuma umarci shugabannin sassan kwamitin da su tuntuɓi sauran ‘yan jam’iyyar da ba a sanya sunayensu a cikin kwamitin ba, domin su ba da gudunmawarsu wajen yaƙin neman zaɓen.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM