NDLEA TA RUSHE MABOYAR MIYAGUN ƘWAYOYI GUDA SHIDA A HADEJIA

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen Jihar Jigawa, karkashin jagorancin Kwamandan Hukumar CN Hassan Katangana Kabaju, ta yi nasarar rushe maboyar miyagun kwayoyi guda shida a garin Hadejia a tsakanin ranakun 10 zuwa 14 ga Agustan 2026, karkashin shirin musamman mai suna “Operation Restore Order.”
Wuraren da aka kai samame sun hada da Unguwar San Kira, Tsohuwar Kasuwa, Kofar Fada, Reservoir Hadejia, Kasuwar Kuda da kuma Kwanar Prison.
A ranar 10 ga Agusta, jami’an NDLEA sun kama mutane biyar tare da kwato tabar wiwi da wasu nau’ikan miyagun kwayoyi daban-daban. Haka kuma, a ranar 12 ga Agusta, an sake kama wasu mutum uku da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi.
Kwamandan Hukumar na Jihar Jigawa, CN Hassan Katangana Kabaju, ya bayyana cewa manufar wannan samame ita ce kare al’umma daga illar miyagun kwayoyi tare da kubutar da matasa daga fadawa cikin shaye-shaye. Ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da irin wannan aiki har sai an kawar da dukkan maboyar miyagun kwayoyi a fadin jihar.
Hukumar ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa NDLEA bayanan sirri kan masu safarar miyagun kwayoyi domin yaki da wannan matsala cikin hadin gwiwa.



