Hukumar DSS ta kama wani dake nuna kansa a matsayin jam'in ta a Abuja

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama wani mutum mai suna Moferewa Maiye, bisa zargin yin sojan gona a matsayin jami’in hukumar da kuma karɓar kuɗi daga mutane a Abuja.
An kama Maiye ne a wani wurin da ke kusa da mahadar NITEL Junction, kan titin Adetokunbo Ademola Way, Wuse II, Abuja, bayan jami’an DSS sun bi sahunsa.
Rahotanni sun ce a lokacin da aka kama shi, yana sanye da kayan aikin DSS kuma yana ɗauke da bindiga ta bogi, wadda ake zargin ya yi amfani da ita wajen tsoratar da masu ababen hawa da karɓar kuɗi daga gare su.
A yayin bincike, wanda ake zargin ya ce kayan DSS da ke hannunsa na ɗan’uwansa ne, Monday Maiye, wanda ya rasu shekaru da suka gabata.
A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da yi masa tambayoyi domin gano yadda ya mallaki kayan hukumar da kuma tsawon lokacin da ya shafe yana aikata irin wannan zargi.



