Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin jihar jigawa ta ayyana a gobe Alhamis a Matsayin ranar huttun murnar cikar shakarar jihar 35 da kirkira

Usman Muhammad Ismail 0 views
Gwamnatin jihar jigawa ta ayyana a gobe Alhamis a Matsayin ranar huttun murnar cikar shakarar jihar 35 da kirkira

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma'aikatan jihar Alhaji Muhammad K Dagaceri ya fitar, wadda yace an bada hutun ne don yin murnar zagayowar ranar kirkirar jihar daga tsohuwar jihar Kano a ranar 27 ga watan Augutan shekarar 2026.

Gwamnatin ta ce ayyana ranar hutun zai baiwa ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar damar yin tunani tare da gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa ni’imomin da jihar ke samu, da kuma zaman lafiya da haɗin kai.

Kazalika shugaban Ma’aikatan ya ce matakin zai baiwa al’umma damar shiga cikin shirye-shiryen bikin cika shekaru 35 da kuma addu’o’in gama-gari ba tare da wata tangarda ta aiki ba.

Ya kuma buƙaci al’ummar jihar da su yi amfani da wannan rana wajen tunawa da irin ci gaban da Jigawa ta samu tun bayan kafuwarta, tare da yin addu’ar samun kyakkyawar makoma.

Gwamnatin jihar ta jaddada muhimmancin haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa, tana mai cewa wannan mataki na nuna ƙudurin gwamnatin na girmama tarihin jihar tare da ƙarfafa ruhin zumunci da haɗin kai tsakanin al’ummar Jigawa.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM