Kungiyar ’yan Jarida ta Ƙasa reshen Jihar Jigawa, ta ƙaddamar da wasu kwamitocin shirya makon ’Yan Jarida na shekarar 2026

Kungiyar ’yan Jarida ta Ƙasa reshen Jihar Jigawa, ta ƙaddamar da wasu kwamitocin shirya makon ’Yan Jarida na shekarar 2026 da kuma kwamitin bayar da kyaututtuka girmamawa.
Kwamitin farko na shirye-shiryen makon 'yan Jaridar na shekarar 2026 wato Press Week zai kasance ƙarƙashin jagorancin Kwamared Sani Muhammad Gumel, yayin da Aminu Umar Shuwajo zai kasance sakataren kwamitin.
Kwamati na biyu na bada kyautukan girmamawa a lokutan bukukuwan zai kasance Karkashin jagorancin Aliyu Muhammad Dangida sai Auwal Muhammad Kazaure sakatare kuma suke da alhakin zakulowa wadan da suka cancanci a karramawa a ya yin bikin da ake sa ran gudanarwa cikin watan Oktobar wannan shekara ta 2026.
Da yake jawabi, shugaban kungiyar na Jihar Jigawa, Kwamared Isma’il Ibrahim Dutse, ya buƙaci mambobin kwamitin da su yi aiki tare domin ganin an gudanar da bikin cikin nasara.
Kazalika ya kara da cewa bikin na shekarar 2026 shi ne karo na farko da NUJ Jigawa ke shirya Makon ’Yan Jarida, kuma zai samar da dama wajen ƙara ƙwarewar ’yan jarida, yin nazari kan aikin jarida da kuma nuna ƙwarewa da haɗin kai.
Da yake magana a madadin mambobin kwamitin, shugaban kwamitin bayar da kyaututtuka, Kwamared Aliyu Muhammad Dangida, ya godewa shugabancin NUJ bisa amincewa da aka yi da su. Ya yi alƙawarin cewa kwamitin zai yi aiki tukuru domin ganin an shirya bikin da ya dace da martabar NUJ a Jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya.



