Gwamnatin jihar Jigawa ta mayar da ma’aikatan shirin J-TEACH guda 1,200 zuwa ma’aikatan gwamnati masu cikakken matsayi da kuma tsarin fansho
Usman Muhammad Ismail 0 views

Gwamnatin jihar Jigawa ta mayar da ma’aikatan shirin J-TEACH guda 1,200 zuwa ma’aikatan gwamnati masu cikakken matsayi da kuma tsarin fansho.
Gwamnatin ta kuma ɗauki ƙarin matasa 820 aiki karkashin shirin J-TEACH, domin taimakawa wajen rage ƙarancin malamai a makarantun jihar.
Matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na ƙarfafa fannin ilimi da tabbatar da samun isassun malamai a makarantun gwamnati.



