Koma Labarai
Labarai

Tsohon shugaban kasa Obasanjo yace babban kuskuren da ya taba yi a Duniya shi ne daukar Atiku a matsayin mataimaki

Usman Muhammad ismail 0 views
Tsohon shugaban kasa Obasanjo yace babban kuskuren da ya taba yi a Duniya shi ne daukar Atiku a matsayin mataimaki

Tsohon shugaban na Najeriya Chif Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007 ya ce matakin daukar Atiku Abubakar a matsayin matakin shi ne babban kuskuren da ya tafka lokacin gwamnatinsa.

Ya dai yi wannan tsokaci ne a Lagos lokacin da yake amsata tambaya kan wane irin kuskure ya yi lokacin mulkinsa, wadda ya amsa da cewa, kowane shugaba yana yin kuskure lokacin da damar mulki ke hanunsa, amma dai a nasa bangaren zabar Atiku shi ne mafi girman kuskure.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM