Koma Labarai
Labarai

Hukumar tsaron lafiya da Dukiyoyi al'umma ta civil defense reshen jihar Jigawa, ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi da sace kwanukan rufin aluminium a Makarantar koyon Jinya dake Hadejia.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Hukumar tsaron lafiya da Dukiyoyi al'umma ta civil defense reshen jihar Jigawa, ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi da sace kwanukan rufin aluminium a Makarantar koyon Jinya dake Hadejia.

A wata sanar da mai magana da yawun hukumar CSC Badaruddin Tijjani Mahmud ya fitar, wadda ya ce Jami'an hukumar sun cafke waɗan da ake zargin ne a bayan katangar makarantar, inda aka same su da murabba'in mita goma sha uku na kwanukan rufin, wadda ake tsammanin an cire su daga aikin gyaran da ake yiwa makarantar.

Sanar ta kara da cewa binciken farko ya nuna cewa, ɗaya daga cikin waɗan da ake zargin jami'in tsaron makarantar ne, lamarin da ya nuna akwai gibi a tsarin tsaron cikin gida na makarantar.

Kwamandan hukumar ta civil defense a jihar Jigawa, CC Muhammad Kabiru Ingawa, ya ce hukumar za ta ci gaba da ƙarfafa sintiri da tattara bayanan sirri da aiwatar da doka domin kare Muhimman Kadarorin gwamnati da Ababen More Rayuwa.

Ya kuma yi gargaɗi ga masu aikata sata da alata kadarorin gwamnati da sauran ayyukan ta'annati ga tattalin arziki da su daina, yana mai tabbatar da cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukuncin doka.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM