Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Kimiyya da Fasaha na Jihar Jigawa, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ya dakatar da Daraktan Dutse Mega School, Malam Abdullahi Shehu, bisa zargin sakaci da aiki.

Kwamishinan ya dauki matakin ne yayin wata ziyarar bazata da ya kai makarantar domin duba yadda ake gudanar da aikace-aikacen makarantar da kuma bin umarnin gwamnatin jihar.
An umarci Daraktan da ya koma ma’aikatar domin jiran matakin gudanarwa na gaba.
Farfesa Chamo ya nuna rashin jin dadinsa kan wasu kura-kurai da ya gano wajen gudanar da makarantar, yana mai jaddada cewa jarin da gwamnati ke zubawa a harkar ilimi dole ne ya haifar da ingantaccen sakamako.
Haka kuma, ya umarci Daraktan Sabis na Makarantu, Malam Mustapha Abdullahi Ringim, da ya gudanar da bincike kan rahotannin rashin halartar wasu malamai a makarantar tare da daukar matakin da ya dace bisa sakamakon binciken.
Kwamishinan ya kuma duba Dutse Model International School, inda ya sa ido kan ayyukan gyaran ajujuwa da dakunan kwanan dalibai, tare da duba aikin gina bita ta koyar da sana’o’i da fasahohin zamani (TVET).
Ziyarar ta kare a School of Arabic and Islamic Studies, Fathara, Dutse, inda ya duba ajujuwan da aka gyara da kuma sabon yanayin ginin gudanarwar makarantar.
Farfesa Chamo ya yaba da ayyukan gyaran da aka kammala, amma ya bukaci shugabannin makarantu su kara himma wajen inganta ayyukansu domin samar da kyakkyawan yanayin koyarwa da ilmantarwa.
Ya sake jaddada kudirin ma’aikatar na kara tsaurara sa ido da tabbatar da cewa kudaden da gwamnatin Jigawa ke zubawa fannin ilimi suna samar da sakamakon da ake bukata.



