Firaministan Pakistan ya dakatar da ma'aikatan asibitin da gobara ta kashe jarirai 14
Usman Muhammad Ismail 0 views

Firaiministan Pakistan Shehbaz Sharif, ya bayar da umarnin dakatar da manyan jami'an 8 na asibitin da jarirai 14 suka mutu sakamakon gobara a sashen kula da masu haihuwa.
Matakin ya biyo bayan rahoton farko game da tashin gobarar ranar Laraba a CibiyarKula da Lafiya ta Pakistan da ke Islamabad, daya daga cikin manyan asibitocin gwamnati na kasar.
An yi nasarar ceto jariri guda. Wata sanarwa daga ofishin Firaiminista ta bayyana cewa bincike ya gano rashin daukar matakan da suka dace da suka hada da ƙararrawa da sinadaran kashe gobara, har da rashin horo kan yadda ake kashe gobara.



