Koma Labarai
Ilimi

Maryam Ibrahim Dan-Azumi Ta Lashe Gasar Alƙur'ani Ta Duniya a Makkah, Ta Samu Kyautar Naira Miliyan 120

Usman Muhammad Ismail 0 views
Maryam Ibrahim Dan-Azumi Ta Lashe Gasar Alƙur'ani Ta Duniya a Makkah, Ta Samu Kyautar Naira Miliyan 120

Wata 'yar Najeriya daga Jihar Gombe, Maryam Ibrahim Dan-Azumi, ta kafa sabon tarihi bayan ta zama zakara ta farko a rukuni na biyu a gasar karatun Alƙur'ani ta Sarki Abdulaziz karo na 46, wadda aka gudanar a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Maryam ta wakilci Najeriya a wannan babbar gasa ta duniya, inda ta fafata a rukunin da ya shafi haddar Alƙur'ani gaba ɗaya (60 Hizbi), Tajwidi, Tafsiri da kyakkyawar tilawa, kuma ta samu maki 97.70, lamarin da ya ba ta nasara a kan sauran mahalarta daga ƙasashe daban-daban.

Bayan nasarar da ta samu, Maryam ta lashe kyautar da aka kiyasta ta kai Naira miliyan 120, abin da ya ƙara ɗaukaka sunanta da na Najeriya a idon duniya.

Wannan nasara ta Maryam ta zama abin tarihi, domin shekarar 2026 ita ce karo na farko cikin shekaru 46 da aka ba mata damar shiga wannan gasa, kuma ita ce ta zama zakara a wannan sabon babi na tarihin gasar.

Maryam ta fito ne daga Unguwar Herwagana da ke Gombe, inda ta yi haddar Alƙur'ani a makarantar Abubakar Siddiq Community School for Qur'an Memorisation, makarantar da ta bayyana alfaharinta da wannan gagarumar nasara.

Kafin wannan gasa ta duniya, Maryam ta riga ta yi fice a Najeriya. Ta taɓa zama ta farko a gasar Alƙur'ani ta ƙasa karo na 40 da aka gudanar a Maiduguri, inda aka ba ta mota kirar Toyota Corolla sabuwa, kujerar Umrah da sauran kyaututtuka.

Haka kuma, a shekarar 2024, ta zama zakara a gasar Nana Asma'u National Qur'an Recitation Competition, abin da ya nuna cewa tafiyarta ta fara ne daga matakin ƙaramar hukuma zuwa jiha, ƙasa da kuma duniya.

Baya ga ƙwarewarta a Alƙur'ani, Maryam tana karatun Physics Education a matakin ƙarshe a Jami'ar Jihar Gombe, abin da ke nuna yadda take haɗa ilimin addini da na zamani.

Abin ban sha'awa shi ne, 'yar uwarta Hajara Ibrahim Dan-Azumi ita ma ta lashe gasar Alƙur'ani ta duniya a ƙasar Jordan a shekarar 2024, inda aka ba ta mota tare da cikakken tallafin karatun jami'a.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Maryam murna, yana mai cewa nasararta ta kawo wa Najeriya girma da mutunci a duniya.

Shi ma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa Maryam ta nuna irin ingancin tarbiyya da ilimin da jihar ke da shi, tare da alƙawarin karrama ta da zarar ta dawo gida.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM