AN BUKACI IYAYE SU JAJIRCE WAJEN TURA 'YA'YANSU MAKARANTA A JIHAR JIGAW

Shugaban Hukumar Ilimin Matakin Farko ta Jihar Jigawa, Farfesa Haruna Musa, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da iyaye mata daga ƙananan hukumomin Roni, Gwiwa, Yankwashi da Kazaure.
Farfesa Haruna Musa ya ce Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, na ware kaso mafi tsoka na kasafin kuɗin jihar domin bunƙasa ilimi, don haka ya zama wajibi malamai, iyaye da sauran al'umma su ba wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati cikakken goyon baya.
Ya ƙara da cewa haɗin kan iyaye da malamai zai taimaka wajen inganta koyarwa da koyo, tare da tabbatar da makoma mai kyau ga yaran jihar.
A nata jawabin, Kwararriyar Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Ilimin Matakin Farko, Dakta Hauwa Mustapha Babura, ta yi kira ga iyaye mata da su riƙa sanya ido kan yadda koyarwa da koyo ke gudana a makarantun 'ya'yansu.
Ta kuma yaba wa Farfesa Haruna Musa bisa ƙirƙirar ƙungiyar iyaye mata, tana mai cewa ƙungiyar za ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin iyaye da makarantu domin inganta ilimin matakin farko a faɗin Jihar Jigawa.


