Koma Labarai
Ilimi

Shugaban hukumar Islamic Education Bureau (IEB) na Jihar Jigawa, Dr. Mubarak, ya bayyana cewa jihar na da kyakkyawan tarihi a gasar karatun Alƙur'ani Mai Girma

Usman Muhammad Ismail 0 views
Shugaban hukumar Islamic Education Bureau (IEB) na Jihar Jigawa, Dr. Mubarak, ya bayyana cewa jihar na da kyakkyawan tarihi a gasar karatun Alƙur'ani Mai Girma

Dr. Mubarak ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Freedom Radio cikin shirin Barka da Hantsi, inda ya ce nasarorin da Jigawa ke samu sun samo asali ne daga jajircewar mahaddata, ƙwarewar malamai da kuma cikakken goyon bayan Gwamnatin jihar Jigawa ga ilimin addini.

A cewarsa, gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin dukkan kuɗaɗen da suka shafi halartar gasar, tare da samar wa mahalarta duk abin da suke buƙata domin su wakilci jihar yadda ya kamata.

Ya ƙara da cewa Jihar Jigawa ta shafe kusan shekaru tana taka rawar gani a gasar karatun Alƙur'ani ta ƙasa, kuma bayan nasarorin da ta samu a shekarun 2011 da 2014, suna da kyakkyawan fata cewa, idan Allah Ya so, za su sake lashe gasar a bana.

Dr. Mubarak ya yi kira ga al'ummar Jihar Jigawa da su ci gaba da yi wa mahalartan addu'a domin Allah Ya ba su nasara, su dawo gida da kambun gwarzon gasar tare da ci gaba da ɗaukaka martabar jihar a fagen ilimin Alƙur'ani Mai Girma.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM