Koma Labarai
Labarai

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a kash Naira biliyan 46 domin aikin sake shimfiɗa kwalta da kuma gina sabon titin saukar jiragen sama na biyu a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Mallam Aminu Kano da ke Kano.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a kash Naira biliyan 46 domin aikin sake shimfiɗa kwalta da kuma gina sabon titin saukar jiragen sama na biyu a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Mallam Aminu Kano da ke Kano.

Ministan Sufurin Jiragen sama da Bunƙasa harkokin Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ne ya bayyana hakan ya yin bikin ƙaddamar da sabon ginin tashar jiragen sama ta cikin gida ta Muhammadu Adamu Dankabo da aka gyara tare da inganta ta a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, a ranar Talata.

A cikin wata sanarwa da Tunde Moshood, Mai Bai wa Ministan Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Sadarwa ya fitar, Ministan ya bayyana cewa wannan aiki na daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin Shugaba Tinubu ke aiwatarwa domin bunƙasa filin jirgin. Ya ce ana sa ran aikin zai ƙara inganta yadda ake gudanar da ayyukan filin jirgin tare da ɗaga martabar Filin Jirgin Sama na Kano zuwa sahun manyan filayen jiragen sama na duniya.

Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ware Filin Jirgin Sama na Kano domin gudanar da manyan ayyukan ingantawa sabo da muhimmancin da filin jirgin yake da shi.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM