Koma Labarai
Labarai

Hukumar Wayar da Kai ta Kasa, NOA, ta yi Allah-wadai da halayen wasu jami’an ’yan sanda

Usman Muhammad Ismail 0 views
Hukumar Wayar da Kai ta Kasa, NOA, ta yi Allah-wadai da halayen wasu jami’an ’yan sanda

Hukumar Wayar da Kai ta Kasa, NOA, ta yi Allah-wadai da halayen wasu jami’an ’yan sanda da aka gani a wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, inda ake zarginsu da neman cin hanci daga wani direba bayan sun kammala binciken motarsa.

Hukumar ta ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne furucin da ake zargin daya daga cikin jami’an ya yi, inda ya ce da direban ya kasance dan kabilar Igbo ne, da ya mare shi.

NOA ta bayyana cewa irin wannan magana ta saba wa ka’idojin hadin kan kasa, mutunta juna, adalci da kuma darajar kowane dan Najeriya ba tare da la’akari da kabila, addini ko ra’ayin siyasa ba.

Hukumar ta yaba wa rundunar ’yan sandan kasar nan bisa gaggawar daukar mataki, inda ta bayar da umarnin cafke jami’an da abin ya shafa tare da fara bincike da matakan ladabtarwa a kansu

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM