JSSSEB Ta Haramta Bikin Kammala Karatu Bayan Jarabawar Sakandare a Jigawa

Hukumar Kula da Ilimin Makarantun Sakandare ta Jihar Jigawa (JSSSEB) ta haramta shirya bukukuwan kammala karatu da liyafa da makarantun sakandare ke yi bayan kammala Jarabawar Kammala Sakandare (SSCE) da ta Hukumar Shirya Jarabawar NECO.
Hakan na kunshe ne cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 17 ga Yuli, 2026 wadda aka aika wa dukkan shugabannin makarantu, masu makarantu masu zaman kansu da daraktocin makarantu a faɗin jihar.
A cewar Hukumar, daga yanzu an umarci dukkan makarantu da su daina shirya, halarta ko tallata bukukuwan kammala karatu da sauran irin waɗannan bukukuwa ga ɗaliban da suka kammala karatun sakandare.
Hukumar ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon ƙaruwar yadda wasu ɗalibai ke gudanar da jerin gwano ba tare da izini ba, suna tayar da hankalin jama'a da kuma aikata wasu halaye na rashin ɗa'a da suka shafi irin waɗannan bukukuwa.
JSSSEB ta yi gargaɗin cewa duk makarantar da aka samu tana shirya ko ƙarfafa gudanar da irin waɗannan bukukuwa saɓanin umarnin da aka bayar za ta fuskanci matakan ladabtarwa da na gudanarwa bisa ƙa'idojin Hukumar.
Hukumar ta buƙaci shugabannin makarantu su tabbatar da cikakken bin wannan umarni tare da ba da haɗin kai domin tabbatar da ɗa'a, zaman lafiya da kuma kare martabar tsarin ilimi a Jihar Jigawa.
Takardar ta samu sa hannun Mansur Ubale, Mataimakin Daraktan Ayyukan Makarantu, a madadin Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Makarantun Sakandare ta Jihar Jigawa.

