JAMI'AR TARAYYA TA DUTSE (FUD) TA LASHE KYAUTAR GIRMAMAWA TA JAMI'A MAFI KYAU A NAJERIYA A SHEKARAR 2026

Ƙungiyar bayar da kyaututtukan ƙwarewa a fannin ilimi ta Najeriya (Nigeria Academic Excellence Award Organisation), mai hedikwata a Legas, ta sanar da cewa Mataimakin Shugaban Jami'ar Tarayya ta Dutse (FUD), Farfesa Ahmad Muhammad Gumel, ya lashe kyautar Mataimakin Shugaban Jami'a Mafi Ƙirƙira da Sabbin Dabaru a Shekarar 2026, a fannin koyarwa ta yanar gizo da ilimin zamani na dijital (E-Learning and Digital Education).
Haka kuma, Jami'ar Tarayya ta Dutse ta samu kyautar Jami'ar Gwamnatin Tarayya Mafi Kyau a Shekarar 2026, a fannin ƙwarewar ilimi da bunƙasa harkokin ilimi.
Bugu da ƙari, jami'ar ta kuma lashe kyautar Jami'ar Gwamnatin Tarayya Mafi Ƙirƙira da Sabbin Dabaru a fannin koyarwa ta yanar gizo da ilimin zamani na dijital.
A cikin wasiƙar sanar da Mataimakin Shugaban Jami'ar nasarar, ƙungiyar NAEA ta bayyana cewa, bayan gudanar da cikakken tantancewa, nazari da tantance sunayen waɗanda aka zaɓa, ƙarƙashin kwamitin ba da shawarwari na NAEA 2026 da kuma kwamitin alkalai masu zaman kansu, an kammala tantancewar tare da tabbatar da cewa Jami'ar Tarayya ta Dutse da Mataimakin Shugabanta sun samu nasara a waɗannan rukunan kyaututtuka:
Jami'ar Gwamnatin Tarayya Mafi Ƙirƙira a Shekarar 2026 – a fannin koyarwa ta yanar gizo da ilimin dijital.
Jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Shekara – a fannin ƙwarewar ilimi da bunƙasa harkokin ilimi.
Mataimakin Shugaban Jami'ar Gwamnatin Tarayya Mafi Ƙirƙira a Shekarar 2026 – a fannin koyarwa ta yanar gizo da ilimin dijital.
A cewar ƙungiyar NAEA, waɗannan kyaututtuka an ƙaddamar da su ne domin karrama gagarumar nasarar da jami'ar ta samu, gudummawar da take bayarwa da kuma jajircewarta wajen inganta ƙwarewar ilimi da taimakawa wajen tsara makomar manyan makarantu a Najeriya.
An tsara gudanar da bikin miƙa kofunan yabo da takardun shaidar lashe kyaututtukan ga Mataimakin Shugaban Jami'ar a birnin Legas a watan Nuwamba.
Wannan babbar nasara ce da ke ƙara fito da Jami'ar Tarayya ta Dutse a matsayin ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ilimi a Najeriya. Muna taya shugabannin jami'ar, ma'aikata, ɗalibai da sauran al'ummar jami'ar murnar wannan gagarumar nasara.



