Shugaba Tinubu ya amince da biyan alwashi na tsawon Rayuwa ga tsofin manyan shugabannin hukumar lura da shige da fice.

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kawo ƙarshen tarin bashin karin girma da aka samu a hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar, tare da amincewa da biyan albashi na tsawon rayuwa ga tsofaffin Manyan Kwanturololi Janar da Mataimakan nanyan Kwanturololi na hukumar lura d Shige da Fice.
Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne a wajen bikin rufe horo na musamman kan tsarin kula da iyakokin ƙasa da harkokin shige da fice, wato Border Control and Immigration Management System, wadda ya gudana a hedikwatar Hukumar Shige da Fice da ke Abuja.
Kazalika Ministan ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa matakan da ya ɗauka na warware matsalar tsaikon karin girma, inda ya bayyana cewa aƙalla jami’ai dubu hamsin ne suka samu karin girma da kuma sababbin muƙamai cikin shekaru uku.
Ya kuma ce shugaban ƙasar ya ƙara yawan ɗaukar sabbin ma’aikata aiki, inda a yanzu aka samu damar ɗaukar sabbin jami’ai da ba su gaza dubu arba’in a lokaci guda ba.
Haka kuma, Tunji-Ojo ya yaba wa shugaban ƙasar bisa jajircewarsa wajen inganta jin daɗin jami’an da ke aiki da kuma waɗanda suka yi ritaya.
Ya bayyana cewa daga cikin matakan da aka ɗauka akwai ƙara yawan fansho ga tsofaffin Manyan Kwanturololi Janar na Hukumar Shige da Fice, domin inganta rayuwarsu bayan kammala aikinsu na gwamnati.



